Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya amince da dakatar da wasu manyan jami’an Cibiyar Gyaran Halin Kangararrun Yara a jihar, dake Babbar Ruga, biyo bayan rahoton kwamitin da aka ɗorawa alhakin gudanar da bincike kan zargin azabtar da wani Matashi dake cibiyar Usman Musa (Abba Bujawa).
Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya fitar, ɗauke da sa-hannun sakataren Yaɗa Labaran sa Abdullahi Aliyu Yar’adua, wadda ta tabbatar da cewa, an dakatar da shugaban cibiyar mai suna Abdulzahir Abubakar da Bala Abubakar, da wani Yunusa Yusuf, saboda rawar da suka taka da ya yi sanadin yanke hannun hagu na wani Usman Musa dake ake kira da Abba Bujawa, da suka tsare sa da kuma ji masa rauni mai tsanani a hannun dama.
Bugu da kari, Gwamnan ya bayar da umarnin korar wani ma’aikacin cibiyar mai suna Murtala Suleiman nan take, saboda hannu a cikin lamarin.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a wani yunƙuri na tausaya wa wanda abin ya shafa, Gwamna Radda ya amince da ba shi kuɗi har Naira N970,000.00 don biyan kuɗin jiyya a Asibiti, da kuma ba shi N35,000,000.00 don yi masa tiyatar hannun da kuma saka masa hannun roba don taimakawa wajen dawo da lafiyarsa.
Haka kuma, Gwamnan ya kuma ya amince da aiwatar da shawarwarin kwamitin da ke da nufin inganta Cibiyar ta Jiha, don haɓɓaka kyawawan ayyuka na ƙasa da ƙasa wajen kula da gyare-gyare da kuma jin daɗin fursunoni.
Kwamitin wanda mai ba da shawara na musamman kan harkokin Gwamnati da sake fasalin ayyuka, Alhaji Usman Isiyaku ke jagoranta, an ba shi umarnin sa ido kan yadda ake aiwatar da dukkan matakan da aka amince da su don tabbatar an bi ƙa’ida da kuma gyara.
Gagarumin matakin dai, na ƙara jaddada kudirin gwamnatin jihar Katsina na tabbatar da kare haƙƙin ɗan Adam, tabbatar da bin doka da oda, da kuma inganta sauye-sauye a dukkan hukumomin jihar.