Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United FC ta ɗauki sabbin ’yan wasa bakwai domin ƙarfafa tawagarta kafin fara kakar NPFL 2025/2026.
Sabbin ’yan wasan sun haɗa da:
Adekunle Samuel, Philip Ogwuche, Uche Collins, Adiku Moses, Bashir Usman, Innocent Arigu, da Azeez Falolu.
Babban mai ba da shawara na ƙungiyar, Azeez Audu, ya ce burin su shi ne lashe kofin gasar ko samun damar zuwa gasa ta nahiyar Afirka.
Za su fara kakar ne da karawa da Warri Wolves a filin Muhammadu Dikko Stadium, a watan Agusta.