Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina tare da haɗin gwiwar jami’an sojoji, rundunarJami’an tsaron Cikin gida na KCWC, da ‘yan sa-kai, inda suka daƙile hare-hare Biyu da wasu da ake zargin ‘yanbindiga ne a lokacin da suke shirye-shiryen kai wani hari a ƙauyukan Unguwar Dudu, Yartasha da Buntu a ƙaramar hukumar Faskari, ta Jihar Katsina.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a cewar sanarwar da Mai magana da yawun rundunar ‘Yansanda ta jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, wadda ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta, 2025.
Ya bayyana cewa, bayyana cewa da misalin karfe 3:00 na rana, inda hukumar ‘yansanda ta samu sahihan bayanai daga al’umma cewa wasu ‘yanbindiga ɗauke da makamai suna shirin kai hari ƙauyen Unguwar Dudu. Nan take, DPO na Faskari ya jagoranci runduna ta jami’an tsaro tare da sojoji da jami’an tsaron al’umma zuwa yankin, ya ce cikin nasara suka tarwatsa ‘yanbindigar kafin su aiwatar da mummunan shirin su.
Haka zalika, da misalin karfe 5:00 na yamma a ranar, rundunar ta sake samun rahoto na wasu ‘yanbindiga da suka mamaye ƙauyukan Yartasha da Buntu da ke yankin Daudawa, inda su ma suka yi yunƙurin kai hari.
Bisa haɗin gwiwa da rundunar sojoji da Jiragen Yaƙi na NAF, jami’an ‘yansanda sun isa wajen da lamarin ke faruwa, inda aka yi artabu da ‘yanbindigar, aka tarwatsa su, aka kuma daƙile harin.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bello Shehu, ya jinjinawa rundunonin tsaro bisa yadda suka mayar da martani cikin lokaci, tare da tabbatar da ci gaba da kokari wajen kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Ya kuma buƙaci hadin kan jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci da wuri domin hana aikata laifuka.