‘Yanbindigar da suka kai hari a ƙalla garuruwa 16 tsakanin Asabar da Lahadi, a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, sun yi ajalin mutane 5 tare da yin garkuwa da Mata da dama.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, a ranar Asabar, ‘yanbindigar sun yi awon gaba da mutane 8 ciki har da Dan Isa, Kyatawa, Tudu, Gidan Haruna, da sauransu, inda suka kashe mutum 1 a Gidan Haruna kuma suka sace mata 8.
A ranar Lahadi kuma, sun sake dawowa Kwalau inda suka kashe mutum 4, Abubakar, Murtala, Aminu da Bello tare da raunata wani Ashafa, wanda aka kai asibitin Kaura Namoda.
Rahotan jaridar Daily Trust, ya ce ‘yan sa-kai sun yi musayar wuta da ‘yanbindigar a daren Asabar, lamarin da ya sa suka ja da baya.
Sai dai, da safe sun dawo cikin shiri, inda suka kai farmaki wajen taron ‘yan sa-kai, inda suka kashe 4, suka raunata 1, tare da sace Mata da kwashe kayan Abinci da na gida.