HomeSashen HausaBama Goyan Bayan Ayyukan Ta'addanci A Najeriya Domin Muma An Kashe Mana...

Bama Goyan Bayan Ayyukan Ta’addanci A Najeriya Domin Muma An Kashe Mana Fulani Sun Fi Dubu 20,000- Miyetti Allah

-

Shugaban ƙungiyar ya kuma ce an sace ma su shanu sun fi Miliyan haɗu cikin shekaru biyar da suka gabata.

Shugaban ƙungiyar Baba Usman Ngelzerma ya bayyana haka, lokacin da yake kare kan su daga zargin cewar basa ɗaga muryarsu a duk lokacin da aka samu ɓatagari daga cikin su dake gudanar da ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Ngelzerma ya ce su kan su Fulani makiyayan ba su tsira daga ayyukan waɗannan ɓatagari ba, domin ko a watannin da suka gabata, an hallaka shugabannin su na jihohin Katsina da Kwara da kuma Filato, saboda haɗa kan da suke yi da hukumomi domin dakile ayyukan ta’addanci a jihohin da suke shugabanci.

Shugaban ƙungiyar ya ce tabbas wannan matsala ta ayyukan ta’addanci ta ɓatawa Fulani suna a Najeriya, amma kuma ba dukkan su ke cikin wannan aiki ba, domin akwai Fulani na gari dake gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali, ba tare da goyan bayan ta’addancin ba.

Ngelzerma ya ce yanzu haka tsakanin Fulani makiyaya dubu 15,000 zuwa 20,000 suka fice daga Najeriya zuwa wasu ƙasashe domin tsira da rayukan su da kuma dukiyoyin su daga waɗannan ƴan ta’adda da suka hana gudanar da kiwo cikin kwanciytar hankali.

Shugaban ya ce ko a ƴan kwanakin da suka gabata, shanu sama da 10,000 aka kwacewa wasu makiyaya a jihar Kebbi, kana kuma aka kora su cikin gonakin manoma, da zummar haddasa rikici, domin nuna wa duniya cewar Fulani makiyaya ne suka sanya shannun a cikin gonaki, alhali kuwa ɓarayi ne suka kora su ciki.

Ngelzerma wanda ya bayyana cewar suna haɗa kai da gwamnoni da kuma jami’an tsaro wajen ganin an dakile ayyukan ta’addanci, ya bukaci a dinga yiwa Fulanin adalci, musamman ganin yadda su ma suke rasa rayukan su da kuma dukiyoyin su daga waɗannan ɓatagarin dake amsa sunan Fulani.

Shugaban ya yi misali da abinda ke faruwa a jihar Anambra, inda gwamnan jihar ya tabbatarwa duniya cewar ba Fulani ne ke gudanar da ayyukan ta’addanci a jiharsa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Mutane 3 A Tsakiyar Katsina Sun Nemi Miliyan 600 Kuɗin Fansa

Wasu ’yan bindiga da suka sace wasu ma’aurata da ’yarsu yayin wani hari da suka kai a unguwar Filin Canada da ke Sabuwar Unguwa a...

Hanyoyin Da Matasa Ya Kamata Su Bi Domin Gina Rayuwarsu Tun Kafin Tsufa – Inji Ameer Salisu Yaro

Da yake ƙarin haske kan shawarwarin, ya ce ‎lokacin samartaka da ƙuruciya ba kawai mataki ne na rayuwa kaɗai ba, mataki ne wanda ake gina...

Most Popular