Katsina United Ta Doke Kano Pillars Da 1-0 A Muhammadu Dikko Stadium
Katsina United ta samu nasarar doke abokiyar hamayyarta, Kano Pillars, da ci 1–0 a wasan gasar Firimiya lig na Kwararru ta Najeriya da aka fafata a filin wasa na Muhammadu Dikko, cikin garin Katsina.
An buga wasan ne cikin tsananin ƙwarewa da hazaƙa inda bangarorin biyu suka nuna gogwarsu su a fagen kwallon kafa, sai dai mintuna na ƙarshen wasa ne Katsina United ta samu damar zura kwallo ta hannun ɗan wasanta, Azeez Falalu, wanda hakan ya bai wa masu masaukin baƙi nasara.
Magoya baya daga sassa daban-daban na jihar Katsina da Kano ne dai, suka halarci wasan, inda suka nuna farin cikinsu ko da yake sakamakon bai yi ma wasu dadi ba.
Hukumar gudanar da wasa ta tabbatar da cewa wannan nasara ta Katsina United zai ƙara mata maki a teburin gasar, yayin da Kano Pillars za ta sake ƙoƙari a wasanta na gaba.