Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aika sunayen mutane biyu zuwa Majalisar Dokokin Kano domin tantancewa a matsayin sabbin Kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa ta jiha.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, gwamnan ya gabatar da sunayen Barrister Abdulkarim Kabir Maude daga Minjibir, wanda zai karÉ“i matsayin Babban Lauya na S (SAN) a gaban kotun koli gobe, da kuma Dr. Aliyu Isa Aliyu, Farfesa a fannin lissafi daga jami’ar North West U, Kano.
Barr. Maude, mai shekara 40, ya yi fice a harkar shari’a inda ya yi aiki fiye da shekara goma, kuma yana da digiri daga jami’o’i daban-daban ciki har da Jami’ar ABU Zaria da BUK.
Shi kuwa Dr. Aliyu, mai shekara 41, ya kware a fannin lissafi inda ya yi karantu a Najeriya da Jordan da Turkiyya, kuma yanzu haka shi ne Darakta Janar na Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano.
A wani ɓangare, Gwamna Yusuf ya kuma amince da nadin Barrister Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Babban Lauyan jiha (Solicitor-General) da Babban Sakataren na Ma’aikatar Shari’a ta Jiha.
Gwamnan ya ce shigar da sabbin mambobin majalisar zartarwa na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke É—auka domin tabbatar da cancanta da kwarewa da gaskiya a aikin gwamnati.