HomeSashen HausaƘasar Indonesia Ta Dakatar Da Lasisin Manhajar Tiktok Saboda Ƙin Bada Bayanai

Ƙasar Indonesia Ta Dakatar Da Lasisin Manhajar Tiktok Saboda Ƙin Bada Bayanai

-

Ƙasar Indonesia Ta Dakatar Da Lasisin Manhajar Tiktok Saboda Ƙin Bada Bayanai

Gwamnatin Indonesia ta dakatar da lasisin gudanarwar manhajar Tiktok a ƙasar, bayan kamfanin ya ƙi bayar da bayanan ga Gwamnati wanda ta nema dangane da zanga-zangar nuna adawa da gwamnati waddda aka gudanar a baya-bayan nan.

Ma’aikatar Sadarwa da Harkokin Dijital ta Indonesia ta bayyana hakan a ranar Juma’ar cewa wannan mataki ya zama dole ne saboda ƙin bin ƙa’idar da ke wajabta wa kamfanonin sadarwa bayar da bayanai idan hukumomi suka buƙata.

Indonesia na daga cikin manyan ƙasashe masu amfani da TikTok a duniya, musamman tsakanin matasa. Wannan mataki zai iya shafar harkokin sadarwa da kasuwancin yanar gizo a kasar, inda daruruwan dubban ‘yan kasuwa ke amfani da TikTok wajen tallata kayayyaki da kuma mu’amala.

Kafar Reuters ta Bayyana cewa hukumomin sun tabbatar da dakatarwar za ta ci gaba da wakana har sai an cimma matsaya tsakanin gwamnati da kamfanin TikTok, kan yadda za a gudanar da musayar bayanai da kuma bin ƙa’idojin tsaro na ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.   Shafin jaridar Zagazola...

Most Popular