HomeSashen HausaNSCDC, Rundunar ‘Yan'sanda Da DSS, Sun Jaddada Cigaba da Hadin Gwaiwa Don...

NSCDC, Rundunar ‘Yan’sanda Da DSS, Sun Jaddada Cigaba da Hadin Gwaiwa Don Yaƙi Da Aikata Laifuka A Jihar Katsina

-

NSCDC, Rundunar ‘Yan’sanda Da DSS, Sun Jaddada Cigaba da Hadin Gwaiwa Don Yaƙi Da Aikata Laifuka A Jihar Katsina

Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) reshen jihar Katsina da takwarorinta na Rundunar ‘Yansanda (NPF) da Hukumar Tsaro ta DSS sun sake jaddada ƙudurorinsu na yin aiki tare domin kawar da laifuka da aikata miyagun ayyuka a fadin Jihar.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, yunkurin jaddada ya biyo bayan wata ziyarar ban girma da Kwamandan Jihar, AD Moriki Acti, Anim ya kai wa Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bello Shehu, da Daraktan DSS na Jihar, Musa Muhammad Yankari, a hedikwatocinsu da ke Katsina.

A jawabinsa, Kwamanda Moriki ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne domin ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin NSCDC da sauran hukumomin tsaro, tare da neman ci gaba da haɗin kai da fahimtar juna.

“Ziyarar yau ba wai neman haɗin kai muka zo ba, amma domin ƙarfafa dangantakar da tuni ta riga ta kasance tsakanin NSCDC da hukumarku,” in ji Kwamanda Moriki.

Ya kuma bayyana godiya bisa tarbar da suka samu daga hukumomin biyu, tare da taimakon da suke baiwa hukumar a cikin Jihar. Ya jaddada cewa kokarin yaƙi da laifi a Jihar Katsina zai fi samun nasara idan kowa ya haɗa hannu wajen tabbatar da tsaron jama’a, kare rayuka, da kuma kiyaye muhimman kadarori da ababen more rayuwa na gwamnati.

A martaninsu daban-daban, Kwamishinan ‘Yan Sanda da Daraktan DSS sun tarbi sabon Kwamanda zuwa Katsina tare da nuna farin ciki da ziyarar tasa. Sun kuma sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da gina kyakkyawar dangantaka ta aiki tare da NSCDC a cikin Jihar.

Bayanin hakan na ƙunshe acikin wata sanarwa da Jami’in hulda da Jama’a na hukumar SC Buhari Hamisu ya fitar a katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Masu Ƙwacen Waya Sun Hallaka Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza...

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Most Popular