Al’umma daban-daban da suke a garin Danmusa dake jihar Katsina, sun zargi Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa, da sama da faɗin da kuɗaɗen su na ƙin kammala aikin Dam a ƙaramar hukumar da kuma Kwangilar babban tankin ruwa a garin Yantumaki da zai ba da ruwa a garin.
Sun bayyana haka ne a ranar Lahadi 05 ga watan Oktoba na shekarar 2025, a lokacin da suke ganawa da Manema Labarai.
Da yake jawabi ga Manema Labarai, Abdulmutallib Dogon Gida, ya ce sun zargi Tsohon sakataren gwamnatin jihar, Dr. Mustapha Inuwa, kan ƙin kammala gwangilar aikin Dam na ƙaramar hukumar Danmusa, da Hon. Sada Soli ya ba shi.
A cewar sa, ba aikin gwangila ɗaya ba ce ke bai kammala ba, har da gwangilar Babban tankin ruwa da ke garin ‘Yantumaki na ƙaramar hukumar.
Ya yi nuni da cewa, rashin kammala aikin asarar gonaki ya ja ma su, wanda ya jaddada cewar ko hakkin su ba a ba su ba na diyyar su kafin a fara aikin tunda farko.
Shi ma da tofa albarkacin bakinsa, Comrade Saifullahi Kabir Danmusa, ya ce rashin kammala aikin ya taɓa ma sa zuciya sosai, inda ya ce tunda an samu tsaro a ƙaramar hukumar, ya kamata a zo a kammala ma su aikin idan kuma ba za a kammala ba a maida ma Gwamnati kuɗin ta.
Ya ƙara da cewa, babu abinda garin Ɗanmusa suka sani baya ga Noma da Kiwo, wanda idan aka kammala aikin za su kara samun kuɗaɗen shiga da kuma yawaitar tattalin arziki a ƙaramar hukumar.
Shi ma da yake kokawa kan ƙin biyan su kuɗaɗen diyyar gonakin su, tare da ƙin kammala ayyukan Dam ɗin, Musa Tanimu Danmusa, inda ya bayyana cewa, sama da mutane 15 ne da ba a ba su kuɗaɗen diyyar ba.
Tuni dai ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a kan ya shiga lamurran su gameda tabbatar waɗanda aka ba aikin sun kammala bi sa aiki mai inganci.
Kafin wallafa rahoton, Wakilin Nigerian Post, ya kira Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa, ta wayar Salula amma bai same shi ba, sai de ya tattauna da Mai taimaka ma sa a kan harakokin Yaɗa Labarai, Anas Suleiman Kbai, inda ya ce bai san da lamarin ba.
Kazalika, mun tattauna da Mataimaki ga tsohon sakataren gwamnatin jihar, Aminu Tsagero, yayin da ya yi nuni da cewa, bai da labarin abinda ake tambayar sa a kai.