HomeSashen HausaHukumar SSS Za Ta Ladabtar Da Jami’an Ta Da Su Ka Kama,...

Hukumar SSS Za Ta Ladabtar Da Jami’an Ta Da Su Ka Kama, Tare Da Tsare ‘Yanjarida A Plateau

-

Hukumar Tsaro ta farin kaya (SSS) ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan jami’an da suka kama kuma suka tsare ’yan jarida biyu na gidan rediyon Jay 101.9 FM a Jos, Jihar Filato.

 

Premium Times ta rawaito cewa ƴan jaridar, Ruth Marcus da Keshia Jang, sun shiga hannu ne yayin da suke yada rahoto kai tsaye kan rikici tsakanin jami’an SSS da limamai a cocin COCIN, inda ake jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nantawe Yilwatda.

 

Shugaban SSS, Adeola Ajayi, ya bayar da umarnin ladabtar da jami’an bayan tabbatar da cewa an saki ’yan jaridar, tare da kiran abin da ya faru “kuskure.”

 

Lamarin ya jawo cece-kuce daga kungiyoyin kare hakkin ’yan jarida da suka bayyana kamun a matsayin take hakkin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanada.

 

An rawaito cewa an riga an gano jami’an da ke da hannu a lamarin, kuma hukumar ta fara ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.   Shafin jaridar Zagazola...

Most Popular