HomeSashen HausaWani Lokaci Mukan Samu Jarirai Mata Na Yin Jinin Al’ada— Likitar Yara

Wani Lokaci Mukan Samu Jarirai Mata Na Yin Jinin Al’ada— Likitar Yara

-

Wani Lokaci Mukan Samu Jarirai Mata Na Yin Jinin Al’ada— Likitar Yara

Wata likitan yara, Ayobola Adebowale, wanda aka fi sani da Your Baby Doctor, ta bayyana cewa wasu jarirai mata na iya fuskantar ɗan zubar jini bayan haihuwa — abin da ake kira da pseudo menstruation ko neonatal menstruation a fannin likitanci.

Jaridar PUNCH ta rawaito Adebowale na bayyana hakan a wani bidiyo da wakilin jaridar Punch ya samu a ranar Asabar, inda ta ce wannan yanayi yana faruwa ne sakamakon canjin kwayoyin halitta (hormones) bayan haihuwa, kuma ba cuta ba ce.

A cewarta, “Jaririyarki na iya yin al’ada bayan haihuwa, kuma wannan shi ne abin da ake kira pseudo menstruation ko neonatal menstruation. Yana faruwa ne saboda yayin da jaririyar ke cikin mahaifiyarta, tana samun tasirin kwayoyin halittar uwa sosai.

“Amma lokacin da aka haife ta, sai kwayoyin halittar suka ragu kwatsam, wanda ke haifar da abin da ake kira withdrawal bleeding — wato kamar al’ada. Wannan yana faruwa ga jarirai mata, kuma abu ne na dabi’a.”

Likitar ta shawarci iyaye kada su firgita idan suka ga irin wannan jini ko ruwa a wajen jariransu.

Ta ce, “Babu dalilin firgita. Ba abin damuwa ba ne. Ku lura da fitar jinin, kuma bayan ‘yan kwanaki zai tsaya da kansa. Ba sai an yi wani abu ba, kuma wannan jariri ba aljani ba ne.”

Binciken likitanci ya tabbatar da cewa wasu jarirai mata na iya yin abin da ake kira neonatal menstruation ko pseudomenstruation, wanda ke faruwa a cikin mako na farko bayan haihuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.   Shafin jaridar Zagazola...

An Fara Binciken Tsohon Gwamna Daga Kudanci Kan Zargin Kitsa Juyin Mulki A Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa ana binciken wani tsohon gwamna daga ɗaya daga cikin jihohin kudancin Najeriya bisa zargin alaƙa da wasu jami’an soji 16 da...

Most Popular