HomeSashen HausaTinubu Ya Yafewa Maryam Sanda Bayan An Yanke Ma Ta Hukunci Kisa...

Tinubu Ya Yafewa Maryam Sanda Bayan An Yanke Ma Ta Hukunci Kisa A 2020

-

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa — matar da aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Maryam Sanda, mai shekaru 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas tana tsare a gidan gyaran hali na Suleja kafin wannan afuwa daga shugaban ƙasa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan shawarar kwamitin shugaban ƙasa kan yafewa fursunoni da masu laifi bayan nazarin takardun shari’arsu da yanayin da suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular