HomeSashen HausaWani Masoyi Ya Ƙone Tsohuwar Budurwarsa Cikin Barikin Sojoji A Oyo

Wani Masoyi Ya Ƙone Tsohuwar Budurwarsa Cikin Barikin Sojoji A Oyo

-

Rundunar ‘Yansandan Jihar Oyo ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruq, da ake zargi da ƙone tsohuwar budurwarsa bayan dangantakarsu ta lalace.

Jaridar PUNCH ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a wani barikin soja da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, wanda ya wallafa bayanai kan lamarin a shafin X , ya bayyana cewa wanda ake zargin ya ce shi da wadda abin ya shafa sun yi alkawarin cewa ba za su taɓa rabuwa ba.

Sai dai, bayan soyayyarsu ta lalace, an ce Faruq ya fusata ƙwarai, inda daga bisani ya zuba wa budurwar mai sannan ya banka mata wuta.

Bayan faruwar lamarin, wasu sojoji da ke cikin barikin sun ceto matar tare da garzaya da ita asibiti, kafin daga bisani su kama wanda ake zargin.

Makama ya rubuta cewa: “Wadda abin ya faru da ita, Omolola Hassan, an ce an zuba mata mai sannan aka ƙone ta da wuta, bayan wanda ake zargin ya fusata kan yadda soyayyarsu ta zo karshe.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ta wayar tarho a ranar Alhamis, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Osifeso ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan al’amarin, za zarar sun kammala su tura shi zuwa kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.   Shafin jaridar Zagazola...

Most Popular