HomeSashen HausaBudurwa Ta Hallaka Kanta Saboda Saurayinta Ya Yi Ma Ta Kishiya A...

Budurwa Ta Hallaka Kanta Saboda Saurayinta Ya Yi Ma Ta Kishiya A Jihar Enugu 

-

Wata budurwa mai shekaru 22, mai suna Odama Mary Agado, ta kashe kanta bayan ta gano saurayinta tare da wata mace a jihar Enugu.

 

VANGUARD ta rawaito cewa Mary, ƴar asalin garin Woleche-Ipuole a unguwar Yahe, karamar hukumar Yala ta jihar Cross River, ta sha guba ne.

 

Majiyoyi sun bayyana cewa marigayiyar, wacce ke sana’ar gyaran gashi a Enugu, tana tafiyar da sana’ar ta cikin nasara, har ta sayi mota ta kuma kamawa saurayin nata hayar gida kwanan nan.

 

Wani daga cikin ƴan uwa, wanda aka bayyana da suna Daniel, ya ce ran Mary ya ɓaci bayan ta kai ziyara wajen saurayin na ta a ranar Juma’ar da ta gabata, sai ta tarar da shi tare da wata mace a cikin gidan da ta kama masa haya.

 

“Ta fusata matuka, sannan ta koma gidan da ita ma take haya. A can ta kira mahaifiyarta ta shaida mata abin da ya faru. Ta kuma ce mahaifiyarta ta karbi ƙaddarar duk abin da ya faru da ita, domin za ta kashe kan ta ne kawai,” in ji Daniel.

 

Ya kara da cewa daga baya, sai kiran mahaifiyar aka yi aka sanar da ita cewa ƴar tata ta sha guba kuma an garzaya da ita asibiti.

 

An ruwaito cewa duk kokarin likitoci na ceton rayuwarta bai yi nasara ba, inda aka tabbatar da mutuwarta da yammacin ranar.

 

Daga bisani aka dauki gawarta zuwa garinsu na Yala, inda aka binne ta a ranar Asabar.

 

VANGUARD ta rawaito cewa dangin Mary ba su kai rahoton lamarin ga ƴansanda ba, suna mai jaddada cewa ita ce ta kashe kanta ba gaira ba dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.   Shafin jaridar Zagazola...

An Fara Binciken Tsohon Gwamna Daga Kudanci Kan Zargin Kitsa Juyin Mulki A Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa ana binciken wani tsohon gwamna daga ɗaya daga cikin jihohin kudancin Najeriya bisa zargin alaƙa da wasu jami’an soji 16 da...

Most Popular