HomeSashen HausaMasu Ƙwacen Waya Sun Hallaka Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Masu Ƙwacen Waya Sun Hallaka Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

-

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa.

Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki.

“A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”

“Bayan na tura mata kudi, kiranmu na ƙarshe shi ne lokacin da ta bar wajen sayar da maganin kusan ƙarfe 6 na yamma. Daga nan ban sake samun ta ba.”

“Na ci gaba da kiranta har zuwa safiyar ranar Lahadi, sai na ɗauka cajin wayarta ne ya ƙare.”

Idris, wanda ya farfado daga suma a ranar Talata bayan girgizar da lamarin ya haifar, ya ce daga baya ya gano cewa marigayiyar ta hau babur din haya kusan ƙarfe 6:30 na yamma a ranar Asabar, amma daga bisani wasu suka kai mata hari don su kwace wayarta.

“Alamu sun nuna matse hannayenta aka yi, alamar cewa an tilasta mata yayin da ake ƙoƙarin kwace wayar.”

“Sannan an bugi kanta da ƙarfi, inda jini ya taru a kan nata, wanda nake zaton shine ya jawo mutuwarta.”

Idris ya ce bayan ta suma, sai barayin suka sace wayarta suka jefar da ita a gefen titi kusa da filin Idi na Mallawa a Tudun Wada Zariya.

Ya ce wani mai tausayi da ya same ta ya garzaya da ita zuwa wani asibiti, daga bisani aka tura ta zuwa Asibitin Koyarwa na ABU, Shika, inda aka tabbatar da rasuwarta.

Mijinta ya ce Hadiza ta rasu watanni uku bayan rasuwar ’yar uwarta, wadda ta ɗauki ‘ya’yanta uku a matsayin nata.

“Ta bar ‘ya’yanta uku da kuma waɗanda ta ɗauka bayan rasuwar ’yar uwarta.”

A nasa bangaren, Sakataren Asibitin, Abdulkadir Balele Wali, ya ce Hadiza mataimakiyar shugabar sashen haihuwa ce, kuma ta halarci aiki a ranar Juma’a har zuwa yamma.

Ya bayyana ta a matsayin kwararriya, mai himma da sadaukarwa, wadda ta ba da gudunmawa wajen ceton rayukan jama’a.

Sakataren ya ce rasuwarta babban rashi ne ga asibitin gaba ɗaya.

Mansur Hassan, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda a Kaduna, bai samu daga wayar wakilinmu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.   Shafin jaridar Zagazola...

Most Popular