HomeSashen HausaGwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim...

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

-

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da yadda yake mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi Talakawa, ɗaga darajar kasuwanci, inganta ilimi, da kuma inganta Harakokin Kiwon Lafiya da ababen more rayuwa.

Mataimakin shugaban ƙasar, ya bayyana haka a ranar Talata 21 ga watan Oktoba 2025, a yayin da yake ƙaddamar da wasu sabbin ayyuka a jihar tare da buɗe su a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Raɗɗa.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, tunda farko, mataimakin shugaban ƙasar ya yaba tare da jinjina ma Gwamnan jihar, wanda tun a lokacin ya jaddada kowanne Gwamna a Najeriya ya yi koyi da irin sa.

A cewar sa, ba kowanne shugaba ne ba zai rinƙa ayyukan raya ƙasa domin al’ummar sa ba, ya ƙara da cewa abin alfahari ne ga jerin ɗaya daga cikin Gwamna a jam’iyyar APC ya shimfiɗa ruwan ayyuka ga Talakawa.

‎A nasa jawabin, Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana godiya ga mataimakin shugaban ƙasar bisa irin goyon bayan da yake baiwa jihar, yana mai cewa, wannan ziyara ta ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta jiha wajen inganta rayuwar al’umma.

‎Raɗɗa ya kara da cewa, wannan aiki da ake gani, ba kawai gina tituna ko gine-gine ba ne kaɗai, gina makoma ce ga jama’ar Katsina baki ɗaya.

Haka kuma, ya yi nuni da cewa, ‎ziyarar da Shettima ya kawo ta kuma baiwa jama’ar jihar dama su bayyana goyon bayansu ga Gwamnati, inda masu ruwa da tsaki suka bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin matakan Gwamnati na ƙasa da jiha zai taimaka wajen ƙarfafa ci gaban tattalin arziki a Arewa gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular