HomeSashen HausaMa'aikatar Lafiya Tayi Bankwana Da Babban Sakataren Ta, Dr. Ahmed Tijjani Hamza,...

Ma’aikatar Lafiya Tayi Bankwana Da Babban Sakataren Ta, Dr. Ahmed Tijjani Hamza, Bayan Wa’adin Aikinsa Ya Kare A Jihar Katsina

-

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Katsina ta shirya ma Dr. Ahmed Tijjani Hamza, gagarumar liyafa, tare da karramawa, a yayin da yake bankwana da ma’aikatan sashen bayan ya yi shekaru 35 yana gudanar da ayyuka kafaɗa da kafaɗa da su.

Bayan kammala taron, tuni dai Babban Sakataren Dr. Ahmed Tijjani Hamza, ya miƙa ragamar ofishin sa ga Hajiya Safiya Ya’u Yamel, wadda tun da farko ita ce Babbar Sakatariyar Sashen kula da Makarantun lafiya a jihar.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, karramawar da kuma miƙa ragamar kujerar ofishin ya gudana, ranar Laraba 22 ga watan Oktoba 2025 a ɗakin taron Ma’aikatar, inda ya samu halartar shuwagabanni na sassan da ke ƙarƙashin Ma’aikatar da ‘yan uwa da abokan arziki a ɓangare da dama.

Da yake jawabi a lokacin, Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hon. Alh. Hon. Musa Adamu Funtua, ya yaba da jajircewar Dr. Ahmed Tijjani Hamza, kan ayyuka tuƙuru, ya ce bai taɓa aiki da wani Babban Sakatare da ya ji daɗin aiki da shi kamar sa ba.

Adamu Funtua ya kara da cewa, bai taɓa da-na-sanin yin aiki da shi ba ko sau ɗaya, sai de ya ƙara ma sa azama wajen gudanar da ayyukan ci gaban ma’aikatar.

A cewar sa, da ba don dokar aiki ta nuna ba lokacin ajewar sa ya yi ba, da sun ci gaba da aiki tare da shi na jagorantar Ma’aikatar har zuwa wani lokaci mai tsawo saboda jajircewar sa da kuma dadin aiki tare da shi.

Da yake maida jawabi, Babban Sakataren Mai Barin Gado, Dakta Ahmed Tijjani Hamza, wanda yake bankwanan rabuwa da abokan aikin sa, ya bayyana godiya mai tarin yawa kan karramawar da aka yi ma sa gamida da gagarumar walima.

A cikin jawabin Dr. Ahmed Tijjani Hamza, ya jaddada cewa, bankwanan da ya yi da ma’aikatan ba yana nufin har abada ba, zai ci gaba da yin zumunci a tsakanin su har baki iyawar sa.

Ita ma a nata jawabin, Babbar Sakatariyar Manyan Makarantu wadda ta karɓi ragamar ofishin Babban Sakataren, Hajiya Safiya Ya’u Yamel, ta shaidawa al’ummar jihar cewa, za ta ɗora ayyukan alherin da Tsohon Babban Sakataren Mai Barin Gado daga inda ya tsaya.

Haka zalika, ta ce za ta jajirce sosai wajen ganin ta yi aiki tuƙuru fiye da yadda ake tsammani don ci gaban ma’aikatar da ma jihar Katsina baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Masu Ƙwacen Waya Sun Hallaka Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza...

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Most Popular