HomeSashen HausaAn Rufe Jama'ar UMYUK Katsina Sai Baba Ta Gani

An Rufe Jama’ar UMYUK Katsina Sai Baba Ta Gani

-

An Rufe Jama’ar UMYUK Katsina Sai Baba Ta Gani

 

Kungiyoyin Malamai da ma’aikatan Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua (UMYU) a Katsina sun tsunduma yajin aiki “sai baba ta gani” a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba 2025.

 

Rahotanni sun bayyana cewa, yajin aikin ya shafi dukkan Malamai da ma’aikatan jami’ar, sakamakon wasu matsalolin da suke zargin gwamnati ta yi biris da su. Daga cikin korafe-korafen da suka gabatar sun hada da; Rashin ingantaccen jin daɗin ma’aikatan jami’ar, Matsalar kwace ikon gudanar da shafin (portal) na makaranta.

 

Sauran sun hada da Karancin kuɗaɗen gudanarwa, da kuma batun walwalar Ɗalibai.

 

Sai dai a nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina ta yi watsi da korafe-korafen kungiyar, tare da jaddada cewa, tana ci gaba da ƙoƙarin magance dukkan matsalolin da suka shafi jami’ar da cigaban ilimi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Tsare-tsare 3 Da Sojojin Amurka Ke Yi Kan Tunkarar Najeriya– Rahoton NY Times

Tsare-tsare 3 Da Sojojin Amurka Ke Yi Kan Tunkarar Najeriya– Rahoton NY Times Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ta gabatar...

Wata Mata Ta Yi Garkuwa Da Kanta, Tare Da Neman Kuɗin Fansa Daga Mijinta A Edo

Wata Mata Ta Yi Garkuwa Da Kanta, Tare Da Neman Kuɗin Fansa Daga Mijinta A Edo Rundunar ƴansandan Jihar Edo ta kama wata mata mai suna...

Most Popular