Gwamnatin Russia ta yi kira ga shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump da ya san da cewa akwai dokoki a duniya kuma ko wacce ƙasa tana da ikon cin gashin kan ta.
Ta kuma bayyana cewa ta na lura da irin rahotannin da ke cewa Amurka na iya ɗaukar matakin soja a Najeriya, bayan kalaman tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya ce zai iya tura dakarun Amurka domin “kare Kiristoci” a kasar.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Moscow ranar Juma’a, inda ta jaddada cewa Rasha na kira ga Amurka da sauran ɓangarorin da abin ya shafa su bi ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa.
Zakharova ta ce, “Muna bibiyar wannan batu sosai, kuma muna kira da a yi taka-tsantsan tare da mutunta ikon mallakar ƙasa.”
Kalaman nata sun biyo bayan jawabin Trump a ranar 1 ga Nuwamba, inda ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) da ta tsara shirin yiwuwar kai farmaki a Najeriya.
Duk da cewa babu wata sanarwa ta hukuma daga Washington kan lamarin, furucin Trump ya haifar da martani daga ƙasashen waje, ciki har da Moscow, wadda ta yi gargadin cewa duk wani mataki ya zama bisa tsarin doka da girmama ‘yancin kowace ƙasa.
