HomeSashen HausaZa mu ƙarar da 'Yanbindiga a shekara ɗaya idan har Gwamnati za...

Za mu ƙarar da ‘Yanbindiga a shekara ɗaya idan har Gwamnati za ta goya mana baya– inji CJTF

-

Haɗakar Jami’an Tsaron Sa-kai na Ƙasa (CJTF) ta ci alwashin karar da ƴanbindiga da ke addabar wasu sassa na Arewacin Nijeriya a cikin shekara ɗaya take.

 

Farfesa Kailani Muhammad, Shugaban CJTF na Ƙasa ne ya baiyana hakan yayin da Charles Omini, Jakadan Musamman na Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam na Afrika ta Yamma ya mika masa takardar zama ɗan hadaddiyar kungiyar jami’an sa-kai ta Afirka ta Yamma (JTF) a Abuja a ranar Asabar.

 

A cewar Muhammad, da Gwamnatin Tarayya ta ba da ƙarfi tare da tallafa wa CJTF kayan aiki,’ da suka dace to za su murƙushe ’yan bindiga cikin shekara guda.

 

Ya yi kira ga gwamnati da ta ba Civilian JTF goyon bayan da ya dace domin su nuna abin da za su iya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kwankwaso Na Nazarin Hada Kai da Atiku da Obi Domin Shiga ADC

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran New Nigeria People’s Party (NNPP), Sen Rabiu Musa Kwankwaso, na nazarin yiwuwar haɗa kai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa...

Katsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku a Janairu 2026

An bukaci Gidan Rediyon Jihar Katsina da ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin Ƙasa na Inyass na...

Most Popular