A wani rahoto da Nigerian Post ta samu daga Aminiya, an tabbatar da cewa, tsofaffin ma’aikatan (FRCN) Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) sun ce sun shirya gudanar zanga-zanga tsirara a gobe Litinin 8 ga Disamba na shekarar 2025.
Shugaban ƙungiyar, Mista Mukaila Ogunbote, shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce za su shiga zanga-zangar ne domin maƙalewar wasu haƙƙoƙinsu da gwamnati ta gaza biya kamar yadda sakataren kuɗi na ƙungiyar tsofaffin ma’aikatan, Bola Popoola ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas.
Sun jaddada cewa, lamarin ya kai su bango ne shiyasa suke ƙoƙarin gudanar da zanga-zangar ko Gwamnatin tarayya za ta waiwayo a garesu.
Wannan dai, ba shi ne karon farko da ‘yan ƙasa gamida masu aiki a ƙasar ke yawan yin barazana na yin zanga-zanga a Najeriya, wanda ko a makonnin da suka gaba ASSUU ta yi Barazanar tsunduma yajin aiki jim kadan bayan da suka gama jan kunne ga wata zanga-zangar lumana a yankunan ƙasar.
