HomeSashen HausaSojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen Shugaban ’Yan Bindiga, Kallamu, A Jihar Sokoto

Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen Shugaban ’Yan Bindiga, Kallamu, A Jihar Sokoto

-

Sojojin Rundunar 8 Division ta Najeriya a Sokoto sun samu gagarumar nasarar kawar da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a yankin Sabon Birni, Jihar Sokoto.

 

An kashe Kallamu ne a wani samame na musamman da sojoji suka gudanar tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai a yankin Kurawa, da safiyar Litinin.

 

Kallamu, wanda babban na hannun daman shugaban ’yan bindiga Bello Turji ne, ya kasance daya daga cikin wadanda suka addabi al’ummar Sabon Birni da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma tada tarzoma a yankin.

 

Rahotonni sun bayyana cewa an kashe shi ne tare da daya daga cikin manyan masu samar wa Turji da kayan aiki da bayanan sirri, a wani artabu da ya faru da safiyar litinin.

 

Rahotanni sun ce Kallamu, wanda asalinsa daga Garin-Idi a Sabon Birni, ya dawo ne cikin yankin bayan tserewa wani farmaki da sojoji suka kai masa a watan Yunin 2025, inda ake zargin ya shige Kogi domin buya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular