Kwamitin Da Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa domin kula da yara masu barace-barace a kan tituna, da sauran masu gararamba, ya ziyarci mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar,CON.
Kwamitin dai yana a karkashin mai ba Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON Shawara Akan Bunkasa Karkara Da Inganta Rayuwar Al’umma Honorabul Nasir Ahmed Lara.
Da yake magantawa a yayin ziyarar, Shugaban Kwamitin ya ce sun ziyarci Masarautar Daura ne domin neman goyon baya da hadin kan mai martaba Sarkin, domin cimma nasara akan nauyin da ka dora masu.
Alhaji Nasir Ahmed Lara ya bayyana wa mai martaba Sarkin alhakin da aka dora masu, sai ya tabbatar da cewa, zasu yi aiki tukuru wurin ganin an cimma nasara.
Ya yabawa Gwamna Radda akan wannan aiki da aka basu, sai ya ce da izinin Allah zasu baiwa marar da kunya wurin ganin sun sauke nauyin.
Da yake maida jawabi, mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar, ya bayyana kafa kwamitin a matsayin abinda ya zo dai-dai da lokaci, lura da yawaitar mutane da suka fada gararamba akan tituna, a sabili da illar shaye-shaye.
Alhaji Umar Farouk Umar ya sha alwashin cewa, masarautar shi zata baiwa Kwamitin cikakken goyon bayan da ya dace, domin ganin an cimma nasara.
Daga nan sai ya yabawa hangen nesan Gwamna Radda akan kafa irin wadannan kwamitoci na ceto rayuwar al’umma, musamman ma marasa galihu.
