Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Alhaji Abdul-Samad Isyaku Rabi’u, ya bai wa dukkan ma’aikatan kamfaninsa kyautar Naira biliyan 30 a matsayin tallafi bisa jajircewarsu a aikin kamfanin. An bayar da wannan kyauta ne a lokacin bikin ƙarshen shekara da kamfanin ya shirya a birnin Lagos a ranar Asabar da ta gabata.
Irin wannan kyauta ta zama al’ada ga manyan kamfanoni musamman a BUA Group, inda ake yin hakan domin ƙarfafa gwiwar ma’aikata, ƙara musu sha’awa wajen aiki, da kuma ƙirƙirar gasa mai kyau a tsakaninsu. Wannan na taimakawa wajen haɓaka ƙwarewa da samar da ci gaba mai ɗorewa a fannonin masana’antun siminti, abinci da sauran sassa da kamfanin ke gudanar da harkokinsa.
A jawabinsa yayin taron, Alhaji Abdul Samad Rabi’u ya bayyana cewa ma’aikata su ne ginshiƙin nasarar BUA, saboda haka kamfanin zai ci gaba da ba da kulawa da la’ada ga masu nuna jajircewa da amana a wajen aiki. Ya kuma jaddada cewa manufarsa ita ce ganin kamfanin BUA ya zama abin koyi a nahiyar Afirka ta fuskar gudanarwa, ɗorewar tattalin arziki, da kyautata rayuwar ma’aikata.
Wani bangare na taron ya haɗa da karrama ma’aikata da suka nuna bajinta a fannoni daban-daban, inda aka ba su lambobin yabo da kyaututtuka. Ma’aikata da dama sun bayyana farin cikinsu tare da godewa shugaban kamfanin bisa wannan alheri da kulawa da ya nuna.
Kamfanin BUA Group, wanda ke da reshe a fannoni da dama kamar siminti (BUA Cement), sukari (BUA Sugar), abinci (BUA Foods) da man fetur da sinadarai, na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya da samar da ayyukan yi ga dubban matasa a sassan ƙasar.
Wannan kyauta ta biliyan 30 da kamfanin ya bayar ta ƙara tabbatar da matsayin BUA a matsayin ɗaya daga cikin kamfanonin da ke ɗaukar ma’aikata tamkar abokan hulɗa wajen cimma manufofin ci gaba.
