Tuesday, June 16, 2026
HomeLabarai‎‘Yanbindiga Sun Hallaka Mutane 20, Sun Kone Rabin Wani Gari a Katsina

‎‘Yanbindiga Sun Hallaka Mutane 20, Sun Kone Rabin Wani Gari a Katsina

Aƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a garin Doma, dake Karamar Hukumar Faskari, dake cikin Jihar Katsina, bayan da ’yan bindiga dauke da manyan makamai suka kai hari a tsakiyar rana, a ranar Talata.

‎Majiyar Katsina Times ta wallafa a shafinta cewa, harin ya fi shafar manyan shugabannin addini, shugabannin magargajiya da wakilan tsaro, yayin da maharan suka rika harbe-harbe da kone gidaje, shaguna da motoci, lamarin da ya bar mutane da yawa ba tare da matsuguni ba.

‎Har zuwa yanzu, jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani ba, yayin da al’ummar garin ke cikin jimami da fargaba, inda suke kira ga gwamnatocin jiha dana tarayya da su ɗauki matakan gaggawa akan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments