Dakarun tsaron gabar tekun Amurka da ke aiki tare da sojojin ruwan ƙasar, sun kama wani babban jirgin ruwa na Najeriya da ake kira da Skipper, sakamakon yadda ake zargin ana amfani da jirgin wajen satar danyen mai da fashin teku da dai sauran laifukan da suka shafi ƙasa da ƙasa.
A cewar jami’an tsaron Amurka, sun kama jirgin ruwan ne a lokacin da suke aiwatar da wani aikin a ƙarƙashin dokar tabbatar da doka da oda ta ƙasar, wacce shugaba Donald Trump ya sanar.
Hukumomin sun bayyana cewa, a lokacin da aka kama jirgin ruwan na dakon mai, akwai tutar ƙasar Guyana a jikinsa.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, sai dai sashen da ke kula da harkokin jiragen ruwan ƙasar ta Guyana, ya ce ko kaɗan jirgin baya da rijista da su, kuma yana amfani da tutar ƙasar ne ta haramtatciyar hanya.
Ita ma dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Najeriya ta bakin mai magana da yawunta Edward Osagie, ya ce basu da masani kan lamarin a hukumance.
Bayaga hukumar NIMASA, shima shugaban ƙungiyar masu jiragen ruwa ta Najeriya Otunba Sola Adewuni, ya ce baya da wasu gamsassun bayanai kan lamarin.
