Kasar Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya da aka tsare bayan da jirginsu ya yi saukar gaggawa a kasar.
An sako sojojin ne bayan Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aike da wata tawaga karkashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, domin ganawa da Ibrahim Traoré, shugaban gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso, a ranar Laraba.
Wata sanarwa da kakakin Tuggar, Alkasim Abdulkadir, ya fitar ta ce bangarorin biyu sun warware matsalar cikin lumana dangane da matukan jirgin Sojojin Sama na Najeriya da sauran ma’aikatan jirgin.
An tsare sojojin kusan makonni biyu bayan Kungiyar Kasashen Sahel (AES) ta bayyana saukar jirgin a matsayin “aikin rashin kyautatawa da ya saba wa dokokin kasa da kasa”.
Sai dai Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ma’aikatan jirgin sun lura da wata matsalar fasaha da ta sa aka yi saukar kariya a Bobo-Dioulasso, wani birni a Burkina Faso mai filin jirgin sama mafi kusa.
NAF ta kara da cewa saukar jirgin ya kasance bisa ka’idojin tsaro na yau da kullum da dokokin sufurin jiragen sama na kasa da kasa.
