HomeSashen Hausa‎Gwamnan Kano Ya Yabawa Tinubu da Abba Bichi Kan Aikin Titin Wuju-Wuju...

‎Gwamnan Kano Ya Yabawa Tinubu da Abba Bichi Kan Aikin Titin Wuju-Wuju a Kano

-

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matukar godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar da ya bayar na sa hannun Gwamnatin Tarayya domin kammala shahararren aikin titin Wuju-Wuju, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 47.

‎Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

‎Gwamnan ya yi wannan yabo ne yayin da yake jawabi a taron Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 35, inda ya bayyana cewa an fara aikin titin ne tun a shekarar 2013 a zamanin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma ya tsaya cik a tsawon shekaru takwas na gwamnatin Abdullahi Ganduje.

‎Gwamna Yusuf ya bayyana cewa bayan gudanar da cikakken nazari, gwamnatinsa ta nemi taimakon Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da kammala aikin.

‎Ya jaddada cewa bukatar ta samu kulawa cikin gaggawa, inda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da ware Naira biliyan 47 domin kammala aikin titin.

‎Gwamnan ya kuma yi yabo na musamman ga Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kasafin Kudi, Hon. Abubakar Kabir Bichi, inda ya yabawa jajircewarsa, sadaukarwarsa da bin diddigi ba tare da an gajiyawa ba daga Majalisar Tarayya har zuwa Fadar Shugaban Kasa, domin tabbatar da amincewa da kammala aikin.

‎Gwamna Yusuf ya ce Hon. Abba Bichi ya tsaya tsayin daka tun daga matakin gabatar da bukata har zuwa samun amincewar karshe, tare da tabbatar da kare muradun Jihar Kano da amincewa da kammala aikin.

‎Ya bayyana Abba Bichi a matsayin jakada nagari ga Jihar Kano a Majalisar Tarayya, tare da kira ga sauran ‘yan majalisar tarayya daga jihar da su yi koyi da sadaukarwarsa, wakilci mai amfani da kishin kasa, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

‎Gwamnan ya kuma yabawa gudummawar Hon. Abba Bichi wajen samar da muhimman ayyuka ga Kano, ciki har da Cibiyar Taron Kasa da Kasa da ke kan titin Maiduguri da kuma shirin gina filin wasa na zamani a garin Bichi.

‎Haka kuma, Gwamna Yusuf ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya amince da karin manyan ayyuka ga Jihar Kano, kasancewarta jiha mafi yawan jama’a a Najeriya, yana mai jaddada shirye-shiryen gwamnatinsa na hada gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin hanzarta samun ci gaba mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Lokacin Gwamnatin Babana, Sabi’u Tunde Ya Yi Ƙarfin Da Ministoci Tsoron sa Suke– Inji Fatima Buhari

Fatima Buhari, ‘yar fari ga marigayi Muhammadu Buhari, ta ce Tunde Sabiu, tsohon sakataren shugaban ƙasa, yana da babban tasiri a lokacin mulkin mahaifinta ta...

‎Burkina Faso Ta Sako Sojojin Najeriya Da Aka Tsare Bayan Ganawar Tuggar da Traoré ‎

Kasar Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya da aka tsare bayan da jirginsu ya yi saukar gaggawa a kasar. ‎ ‎An sako sojojin ne bayan Shugaban Kasa...

Most Popular