A Najeriya, rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro da fararen hula (JTF) a jihar Zamfara ta sanar da kashe wani shahararren kasurgumin ɗan bindiga, Kacalla Isuhu Buzu, a garin Kaya da ke
yankin ƙaramar hukumar Maradun.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan da al’ummar Kuncin Kalgo da ke ƙaramar hukumar Tsafe suka shiga mawuyacin hali sakamakon hare-haren ‘yan bindiga, inda aka tilasta musu biyan harajin kuɗi naira miliyan 20, tare da sayen babura uku ga maharan.
Kashe Kacalla Isuhu Buzu ya biyo bayan wani farmakin ramuwar gayya da jami’an tsaro suka kai wa ‘yan bindiga a yankin Kuncin Kalgo, bayan korafe-korafen da al’ummar yankin suka yi na yawaitar hare-hare da karɓar haraji ba bisa ka’ida ba.
Wani mazaunin Kuncin Kalgo, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaida wa BBC Hausa cewa al’ummar yankin na ci gaba da rayuwa cikin tsananin fargaba.
“Yanzu haka muna zaune ne cikin matsanancin tashin hankali. Rayuwarmu na cikin barazana saboda ba mu san lokacin da za a sake dawowa ba,” in ji shi.
Har yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani ba kan yadda aka kashe ɗan bindigan, sai dai sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da matsa wa masu aikata laifuka a faɗin jihar Zamfara
