Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin janye jakadan ƙasar daga Najeriya, Richard Mills, a wani bangare na sauyin tsarin diflomasiyya da ya shafi sama da ƙasashe 20 a duniya.
Najeriya na cikin ƙasashe 15 na Afirka da abin ya shafa, tare da wasu ƙasashe irinsu Masar, Senegal, Rwanda, Uganda, Nijar da Kamaru. An kuma aiwatar da matakin a wasu ƙasashen Asiya, Turai da Amurka ta Tsakiya da Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa dukkan jakadun da aka janye an nada su ne a zamanin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden, kuma an sanar da su cewa wa’adin aikinsu zai ƙare a watan Janairu mai zuwa.
Richard Mills ya fara aiki a Najeriya a Mayu na bara, kuma janyewarsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ɗan tangarda a dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka, musamman kan batutuwan biza da tsaro, duk da ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu.
