HomeSashen Hausa‎Zulum Ya Shiga Damuwa Bayan Harin Da Aka Kai Ma Masallata A...

‎Zulum Ya Shiga Damuwa Bayan Harin Da Aka Kai Ma Masallata A Jihar

-

‎Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kakkausar suka kan harin kunar bakin wake da ya auku a masallacin kasuwar Gamboru da ke Maiduguri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 35.

‎Rahotanni sun nuna cewa ɗan kunar bakin waken ne ya kutsa kai cikin masallacin a daidai lokacin da masu ibada ke gudanar da sallar Magariba a daren Laraba, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da jimami.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ya fitar, Gwamna Zulum ya bayyana harin a matsayin mummunan aiki da ke nuna rashin mutunta addini da darajar rayuwar ɗan Adam, yana mai cewa kai hari a wurin ibada “cin zarafi ne ga darajar masallaci a lokacin da bayin Allah ke ibada”.

‎Gwamnan ya bukaci al’umma da hukumomin tsaro da su ƙara sa ido tare da ɗaukar matakan tsaro masu tsauri, musamman a wuraren ibada da kasuwanni, duba da lokacin bukukuwan da ake ciki.

‎Haka kuma, Zulum ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana addu’ar Allah ya jikansu da rahama, tare da fatan samun sauƙin warkewa ga waɗanda suka jikkata.

‎Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace domin hana sake aukuwar irin wannan hari a lokacin bukukuwa da ma bayan haka, yana mai jaddada kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎DA DUMI-DUMI: Rikici Ya Ɓarke A Sabuwar Unguwa Katsina, Mutum 1 Ya Rasu, Matasa Sun Cinna Wuta a Ofisoshin Tsaro

‎A daren jiya zuwa safiyar yau, an samu tashin hankali a Sabuwar Unguwar Kofar Kaura, lamarin da ya janyo hankalin al’umma tare da haifar da...

‎Kwankwaso Ya Bayyana Wadanda Zasu Yi Takarar Zaben Cike Gurbi A Jam’iyyar NNPP

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya amince da bai wa ’ya’yan ’yan Majalisar Jiha biyu da suka rasu, damar tsayawa takara, domin neman...

Most Popular