HomeSashen HausaMun Ji Dadin Haɗin Kan Da Najeriya Ta Ba Mu Wajen Kai...

Mun Ji Dadin Haɗin Kan Da Najeriya Ta Ba Mu Wajen Kai Farmaki A Yankunan Ƙasar– Amurka

-

Sakataren yaƙi na Amurka ya yaba wa gwamnatin Najeriya bisa goyon bayan da ta bayar bayan kai hare-haren bama-bamai kan wuraren da ‘yan ta’adda suke.

 

Sakataren yaƙi na Amurka, Pete Hegseth, ya yaba wa hwamnatin Najeriya saboda haɗin kai da goyon bayan da ta bayar bayan wani harin jirgin yaki da Amurka ta jagoranta, wanda aka kai kan wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne ajihar Sokoto.

 

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa harin na sama, wanda ya faru a ranar Alhamis, ya auku ne a wani wuri da ke kaauyen Jabo a jihar Sokoto.

 

Wannan hari yana cikin wani babban shiri na yaƙi da ta’addanci da gwamnatin Amurka ke aiwatarwa tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya.

 

Sai dai, mazauna garin Jabo sun ce babu wanda ya rasa ransa a harin.

 

A cewar mazauna kauyen, daga baya mutane da dama sun taru a wurin da fashewar ta faru, inda suka tabbatar cewa ba a rasa rai ko guda ba.

 

Da yake mayar da martani game da harin, Mista Hegseth, ta cikin wani sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta, ya ce wannan mataki ya nuna cewa ma’aikatar yaƙi ta Amurka na da shiri tsaf wajen mayar da martani cikin gaggawa kan barazanar ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Abinda Ya Faru Da Ni Ya Zame Min Alkhairi– Malam Bala Dorayi

Malam Bala Dorayi, wanda aka fi sani da Sarkin Yakin Karyar Ƙasar Hausa, ya bayyana cewa abin da ya faru da shi a baya kaddara...

‎Kim Jong Un Ya Zaɓi Ƴarsa Mai Shekara 13 a Matsayin Wadda Za Ta Gaje Shi ‎

Rahotanni daga National Intelligence Service (NIS) sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya zaɓi ƴarsa mai shekara 13, Kim Ju Ae,...

Most Popular