HomeLabaraiJiragen Yaƙin Da Muka Siya Daga Amurka, Za Su Iso Najeriya Nan...

Jiragen Yaƙin Da Muka Siya Daga Amurka, Za Su Iso Najeriya Nan Bada Jimawa Ba- Tinubu

-

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi odar jiragen yaƙi guda huɗu daga Amurka, waɗanda za su iso Najeriya nan ba da jimawa ba, domin ƙara ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro da ta’addanci.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da tawagar kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a gidansa da ke Lagos.

 

Ya ce duk da jinkirin isowar jiragen, gwamnati na ci gaba da neman taimako daga ƙasashen waje, ciki har da Turkiyya.

 

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta kai hare-haren sama kan ‘yan ta’adda a Arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da gwamnatin Najeriya ta tabbatar, tana mai cewa an yi shi ne bisa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

 

Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa shirin kafa ‘yansandan al’umma da na jiha zai zama gaskiya da zarar majalisar dokoki ta Kasa ta kammala gyare-gyaren dokokin da suka dace.

 

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen dawo da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a ƙasar, duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Foil Kidnap Attempt, Rescue 18-Year-Old Girl in Danmusa LG

The Katsina State Police Command has foiled a kidnapping attempt and rescued an 18-year-old girl in Danmusa Local Government Area following a swift response by...

Harin Sojin Sama a Zamfara Ya Hallaka Sama da Mutane 100

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna...

Most Popular