Sojojin Runduna ta 3 da kuma Joint Task Force Operation Enduring Peace (JTF OPEP) sun dakile wani shirin hari da ‘yan fashi dauke da makamai suka yi niyyar kaiwa a Jihar Plateau.
Sojojin sun kuma kashe wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda tare da kwato makamai a yayin aikin.
Bisa sahihin bayanan sirri da aka samu da sanyin safiyar ranar 25 ga Disamba, sojojin sun kaddamar da farmaki a unguwar Gwande da ke Monguna District, karamar hukumar Bokkos.
A wata sanarwa, jami’in yada labarai na aikin, Samson Zhakom, ya ce an tare ‘yan fashin ne yayin da suke shirin kai hari wani gari makwabta, inda aka yi artabu da su.
Ya ce sojojin sun kwato bindiga kirar revolver da aka kera da hannu, bindiga karama (pistol) da aka kera da hannu, harsasai guda tara na 7.62mm, da kuma harsashi (cartridges) guda shida a wurin.
Zhakom ya kara da cewa binciken farko ya tabbatar da cewa dan fashin da aka kashe mamba ne na wata kungiya mai hatsari da ke addabar Gwande da yankunan da ke kewaye.
Bayan wannan artabu, sojojin sun kara kaimi wajen bin sawun sauran ‘yan kungiyar da suka tsere.
Rundunar sojin ta tabbatar wa mazauna Jihar Plateau da kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, tare da rokon jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanan sirri cikin lokaci.
