Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta nuna farin ciki bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da ƙarin albashi da kashi 40 cikin 100 ga malaman jami’o’i, biyo bayan nasarar sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 da aka kulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya.
ASUU ta sanar da cewa an cimma yarjejeniyar ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, lamarin da ya kawo ƙarshen tattaunawar da ta shafe shekaru takwas ana yi tun daga 2017.
Tsawon lokacin tattaunawar ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen duba yarjejeniyar 2009 a shekarar 2012, abin da ya jawo yawan yajin aiki a tsawon shekaru.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar 24 ga Disamba, 2025, ƙungiyar ta ce sabuwar yarjejeniyar an tsara ta ne domin farfaɗo da tsarin jami’o’in gwamnati a Najeriya ta hanyar magance matsaloli da suka daɗe suna addabar fannin, kamar ƙarancin kuɗaɗen tallafi, ‘yancin kai na jami’o’i, ‘yancin gudanar da karatu i (academic freedom), da kuma karuwar ƙauracewar ƙwararru.
Baya ga ƙarin albashin, yarjejeniyar ta kuma ƙunshi inganta sharuddan aiki, sake tabbatar da tanadin fansho ga farfesoshi, sabon tsarin kasafin kuɗi na musamman ga jami’o’i, da kuma shawarwarin kafa Hukumar Bincike ta Ƙasa (National Research Council) wadda za a rika tallafa mata da aƙalla kashi ɗaya cikin 100 na tattalin arziki na Najeriya.
