HomeSashen HausaKoriya Ta Arewa Ta Ƙera Jirgin Ruwa Da Ke Amfani Da Makamashin...

Koriya Ta Arewa Ta Ƙera Jirgin Ruwa Da Ke Amfani Da Makamashin Nukiliya

-

A cewar rahoton da kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta Fitar ta ce jirgin na dauke da makamai Masu linzami masu jagora na dabarun soja.

 

Wannan ci gaba na iya zama babban babbar wajen karfafa karfin rundunar sojin ruwan Pyongyang.

 

Sakamakon matukar wahalar fasahar da ake bukata wajen irin wannan aiki, ba a kawar da yiwuwar samun taimako daga Rasha ba.

 

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya kai ziyara wurin gina sabon jirgin ruwan Mai dauke da nukiliya, inda ya duba ci gaban wasu makaman karkashin ruwa na sirri.

 

An kiyasta nauyin jirgin ruwan ya kai kusan tan 8,700, kuma yana dauke da makamai masu linzami masu jagora na dabarun soja.

 

A cewar bayanin da aka fitar, “Aikin zai kara habaka karfin nukiliyar kasar da kuma kare iyakokinta a teku.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Kwankwaso Ya Bayyana Wadanda Zasu Yi Takarar Zaben Cike Gurbi A Jam’iyyar NNPP

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya amince da bai wa ’ya’yan ’yan Majalisar Jiha biyu da suka rasu, damar tsayawa takara, domin neman...

‎Gwamnatin Tarayya ta Kammala Horas da Sama da Jami’an Tsaron Daji 7,000 a Jihohi 7

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta kammala horas da sama da sabbin jami’an tsaron daji 7,000 da aka dauka aiki daga jihohi bakwai, a wani...

Most Popular