Rundunar Tsaron NSCDC, reshen Jihar Katsina, ta kama mutane 8 da ake zargi da kai hari a Koramar Nayalli da ke Sabuwar Unguwar Katsina.
Hakan na a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SC Buhari Hamisu ya fitar, inda ya bayyana cewa a ranar Lahadi, 28 ga watan Disamba, 2025 da misalin karfe 09:30 na safe, wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka sun kai hari a Koramar Nayalli don nuna rashin jin dadinsu kan aikin sintiri na ‘yan sanda a ranar Asabar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Uzairu (wanda ake kira Dan’kuda), wani sanannen dan daba a unguwar.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a yayin harin, waɗanda ake zargin sun ƙone babura guda 3 da wasu kayan aiki na karamin ofishin hukumar dake a ƙoramar Nayalli, sannan sun kai hari a wasu kananun ofisoshin NSCDC da na ‘yansanda dake a Filin Kanada da nufin lalata wurin. Sai dai tawaga ta musamman ta NSCDC haɗin gwiwa da ‘yansanda ta samu nasarar daƙile lamarin, inda aka samu nasarar dawo da zaman lafiya.
Kwamandan NSCDC na Jihar Katsina, CC AD Moriki, ya ziyarci wurin harin tare da kafa kwamiti mai mutane 7 domin gudanar da cikakken bincike. An kuma kama mutane 8, waɗanda za a bi dukkan matakan shari’a a kansu.
Kwamandan ya yi gargadi ga duk wani mai aikata laifi, masu barnata dukiya da masu cutar da tattalin arziki da su daina aikata laifuka ko su fuskanci hukuncin doka. Haka kuma ya gode wa al’ummar jihar bisa hadin kai, tare da kira ga kowa da kowa da ya taimaka wajen samar da bayanai masu inganci kan tsaro da bayar da kariyar akan kadarorin jama’a.
