Wani jirgin marar matuƙi (drone) ya faɗo a wani daji da ke kusa da garin Kontagora, a Jihar Neja, da yammacin yau Juma’a, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ba tare da jikkata kowa ba, yayin da har yanzu ba a tabbatar da dalilin faɗuwar jirgin ba, Wasu mazauna yankin sun ce sun ji ƙara mai ƙarfi kafin daga bisani suka ga jirgin ya faɗo a cikin dajin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro basu fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da mallakar jirgin ko manufar tashi da aka yi da shi.
Sai dai ana sa ran jami’an tsaro za su fara bincike domin gano musabbabin faɗuwar jirgin da kuma ko akwai wata barazana ga tsaron al’umma.
Hukumomi sun shawarci al’umma da su nisanci yankin da lamarin yafaru, tare da bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali.
Za mu cigaba da bibiyar lamarin tare da kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu.
