HomeSashen HausaTrump Ya Yi Barazanar Kai Wa Masu Zanga-zanga a Iran Ɗauki

Trump Ya Yi Barazanar Kai Wa Masu Zanga-zanga a Iran Ɗauki

-

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya ɗaukar mataki idan hukumomin Iran suka yi amfani da ƙarfin soji wajen murƙushe masu zanga-zangar da ke gudana a wasu sassan ƙasar.

‎Trump ya bayyana hakan ne ta shafinsa na sada zumunta, inda ya ce idan aka ci gaba da kai hari ko kashe masu zanga-zangar da ke fitowa domin nuna ƙin amincewa da halin tattalin arziki da tsadar rayuwa, Amurka “za ta shiga tsakani domin kare fararen hula.”

‎Zanga-zangar ta barke ne a Iran sakamakon matsin tattalin arziki, faduwar darajar kuɗin ƙasar da kuma hauhawar farashin kayayyaki. Rahotanni sun nuna cewa an samu rikici tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane.

‎A martaninta, gwamnatin Iran ta yi watsi da barazanar Trump, tana mai cewa duk wani tsoma bakin ƙasashen waje a harkokin cikin gidan ƙasar ba za a amince da shi ba, kuma hakan na iya ƙara dagula zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

‎Tuni dai masu lura da al’amuran duniya ke ganin wannan furuci na Trump na iya ƙara tsananta dangantakar da ke tsakanin Amurka da Iran, wadda tuni ke cikin yanayi na tashin hankali tun bayan takunkumi da sabanin siyasa da ke tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku a Janairu 2026

An bukaci Gidan Rediyon Jihar Katsina da ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin Ƙasa na Inyass na...

‎Jirgin Marar Matuƙi Ya Faɗo a Dajin Kontagora, Jihar Neja

Wani jirgin marar matuƙi (drone) ya faɗo a wani daji da ke kusa da garin Kontagora, a Jihar Neja, da yammacin yau Juma'a, kamar yadda...

Most Popular