HomeSashen HausaKwankwaso Na Nazarin Hada Kai da Atiku da Obi Domin Shiga ADC

Kwankwaso Na Nazarin Hada Kai da Atiku da Obi Domin Shiga ADC

-

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran New Nigeria People’s Party (NNPP), Sen Rabiu Musa Kwankwaso, na nazarin yiwuwar haɗa kai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023 na Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party (LP) a shekarar 2023 da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, a ƙarƙashin African Democratic Congress (ADC). Wannan na zuwa ne bayan sauya sheƙar Gwamna Kwankwaso, Abba Yusuf, da yawancin ‘yan majalisar jihar Kano zuwa All Progressives Congress (APC).

Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi Rahotanni daga THISDAY, sun bayyana cewa, duk da cewa tsarin siyasar Kwankwaso yana jan kafa zuwa APC, shi da masu goyon bayansa na Kwankwasiyya movement suna tattaunawa da ADC Domin yiwuwar haɗa kai da jam’iyyar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa THISDAY cewa tattaunawar sirri na gudana domin tsara gagarumin haɗin gwiwa kafin zaɓen 2027, duk da cewa akwai alamun ƙarfi cewa Gwamna Abba Yusuf zai sauya sheƙa zuwa APC ranar Litinin, abin da Kwankwaso ya nuna rashin amincewa da shi, wanda ya haifar da rashin jituwa a tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya.

Majiyoyi kusa da Gwamna Yusuf sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima; Shugaban APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe; tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje; da Shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, za su halarci wani gajeren taron murnar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki a Abuja.

Idan tattaunawar tsakanin Atiku, Obi, da Kwankwaso ta cimma nasara, hakan zai iya canza fannin siyasar adawa a Nijeriya gaba ɗaya, tare da sauya lissafin siyasa a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gwamnatin Gombe Ta Bai Wa Iyalan ’Yanjarida 7 Da Suka Rasu Tallafin Miliyan 14

Gwamnatin Jihar Gombe ta raba naira miliyan 14 ga iyalan ’yan jarida bakwai da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a...

‎Gidauniyar Dahiru Mangal, Ta Yiwa Mutane 18,000 Aikin Ido Kyauta A Katsina

‎Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta...

Most Popular