Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar mutane bakwai tare da jikkatar wasu 14 sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya faru a jihar.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, hadarin ya auku ne da yammacin Lahadi a kan titin Chaichai–Ringim, bayan wata arangama gaba-da-gaba tsakanin motoci biyu.
SP Adam ya bayyana cewa hadarin ya faru ne a kauyen Yakasawa da ke Karamar Hukumar Ringim, inda lamarin ya shafi wata mota kirar Golf 3 Wagon da kuma wata mota mai kirar Sienna.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da na agajin gaggawa sun garzaya wurin domin kai dauki, tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa, yayin da aka fara bincike domin gano musabbabin hadarin.
