HomeSashen HausaBa Mu Adawa Da Ma Su Sasanci, Domin Sulhu Ba Rauni ba...

Ba Mu Adawa Da Ma Su Sasanci, Domin Sulhu Ba Rauni ba Ne– Inji Ƙungiyar Civil Society Coalition for Peace a Katsina

-

‎Ƙungiyar Civil Society Coalition for Peace reshen jihar jihar Katsina, ta shirya taron Manema Labarai a Katsina, domin bayyana matsayarta kan shirin sulhu da gwamnatin jihar ke aiwatarwa a ƙoƙarin ta na magance matsalar rashin tsaro.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, taron wanda ya gudana a ranar 15 ga watan Janairu 2026, ya wanzu ne tare da sa-hannun shugaban ƙungiyar ‘yan ƙasa masu fafutukar tabbatar da shugabanci, Comrade Shamsuddeen Na Alhaji, da Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, Sakataren Ƙungiya matasan jihar Katsina, ma su rajin samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa, da Babangida Mai Kuli Abukur, shugaban ƙungiyar RIBACHA, da kuma Hassan Mai Dogon Faci Batsari, shugaban ƙungiyar maido da martabar Arewacin Najeriya, reshen ƙaramar hukumar Batsari.

‎Da yake jawabi ga Manema Labarai, Shugaban ƙungiyar, Comrade Shamsuddeen Salisu Na Alhaji Jibya, ya ce makasudin taron shi ne nuna goyon baya ga matakan Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda, musamman wajen sasanci da masu garkuwa da mutane a wasu yankunan jihar.

‎Ya bayyana cewa, ƙungiyar ta gudanar da bincike mai zurfi, tare da tattaunawa da al’ummar yankunan da abin ya shafa, wanda kuma ta yi nazari kan rahotannin kafafen yaɗa labarai.

A cewar sa, sakamakon binciken ya nuna cewa, shirin sulhun da akai ne ya haifar da sauyi mai ma’ana, inda aka samu damar buɗe makarantu da kasuwanni, tare da raguwar hare-hare, da asarar dukiyoyi da salwantar rayukan jama’a.

Kazalika, ‎shugaban ƙungiyar ya ce, bi sa waɗannan hujjoji ne suka yanke shawarar goyon bayan shirin sulhu, yana mai kuma jaddada cewa, ba sa tare da masu adawa da sasanci. Ya ƙara da cewa addini da zamantakewa duk suna ƙarfafa sasanci, yana mai cewa “wuta dai ba ta kashe wuta.”

‎A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga sauran gwamnatocin jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro da su rungumi hanyar sulhu da sasanci a matsayin wata hanya ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular