Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
Popular Hausa News ta ruwaito cewa Wada Protocol ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa sakatariyar jam’iyyar ADC ta Jihar Katsina, inda ya yanki katin zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC na halas.
A cewarsa, babban dalilin da ya sa ya yanke shawarar sauya sheƙa shi ne canjin manufar tafiyar jam’iyyar APC, inda ya ce jam’iyyar ta kauce daga ainihin akidar da aka kafa ta a kai.
“APC da muka sani a baya ba ita ce ake tafiya da ita a yau ba. An sauya tafiyar, an sauya manufa,” in ji Wada Protocol.
Ya ƙara da cewa tun da farko shi kaɗai ne ya yi niyyar dawowa jam’iyyar ADC, amma daga bisani yaransa suka biyo shi a wannan sabuwar tafiyar.
Da yake tsokaci kan alaƙarsa da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, Wada Protocol ya ce duk da sauya jam’iyya, har yanzu suna cikin kyakkyawar alaƙa, yana mai jaddada cewa siyasa ra’ayi ce, ba dole ta raba abokantaka ba.
“Gwamna Raɗɗa abokina ne kuma aminina ne. Mun shafe fiye da shekaru 30 muna tare a siyasa,” in ji shi.
Wada Protocol ya tuna cewa tun a zamanin marigayi Umaru Musa Yar’adua suna tare a harkokin siyasa, daga baya kuma suka sake haɗuwa a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Aminu Bello Masari, inda ya riƙe mukamai daban-daban har ya kai ga matsayin DG Protocol.
Ya kuma bayyana cewa bai taɓa samun wata matsala tsakaninsa da Gwamna Raɗɗa ba tun lokacin da suke aiki tare, yana mai cewa sun gudanar da ayyuka da dama tare cikin fahimta da jituwa, har zuwa lokacin da ya bar aiki zuwa SMEDAN.
“Ina iya bugun gaba cewa a cikin waɗanda suka tsaya tare da shi, babu wanda ya bada gudunmawa wajen ya zama ɗan takarar gwamna kamar ni,” in ji Wada Protocol.
Ya ƙara da cewa gudunmawa a siyasa ba wai kuɗi kaɗai ba ce, illa ta haɗa da shawarwari, dabaru da tasiri da ke kaiwa ga samun nasara.
Sauya sheƙar Wada Protocol dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa a Jihar Katsina, lamarin da ke ƙara janyo hankulan jama’a da masu sharhi kan alkiblar siyasar jihar nan gaba.
