HomeSashen HausaKamfanin Shell Ya Yi Alƙawarin Zuba Jarin Dala Biliyan 20 A Najeriya...

Kamfanin Shell Ya Yi Alƙawarin Zuba Jarin Dala Biliyan 20 A Najeriya Bayan Dala Biliyan 7 Da Aka Kashe– NNPCL GCEO

-

Shugaban Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mista Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa Kamfanin Shell Petroleum Development Company ya kuduri aniyar neman ƙarin damar zuba jari na kimanin dala biliyan 20 a Najeriya cikin shekaru biyu masu zuwa, bayan sabunta ƙwarin-gwiwar masu zuba jari da gyare-gyaren Gwamnati suka haifar kwanan nan.

Ojulari ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, game da manufar wani ƙudiri da aka gabatar wa Shugaba Bola Tinubu, yana mai nuna tasirin Umarnin Zartarwa da aka bayar a shekarar 2025 don jawo hankalin zuba jari kai-tsaye na ƙasashen waje (FDI) a fannin Mai da iskar Gas na Najeriya.

A cewarsa, Umarnin Zartarwa, wanda aka gabatar bayan aiwatar da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), an tsara su ne don inganta gasa a Najeriya a fannin zuba jarin makamashi a duniya, a tsakanin gasa mai tsauri daga wasu ƙasashen Afirka, Guyana da wasu sassan Gabas Mai Nisa.

A cewarsa: “Gasar saka hannun jari ta duniya ce; kuma wasu ƙasashe suna canza manufofinsu ta hanyar da ta dace don jawo hankalin masu zuba jari. Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da Shugaba Tinubu ya yi shi ne gabatar da Umarnin Zartarwa (Executive Order), wanda ya ƙara wa masu zuba jari ƙwarin-gwiwa”, in ji Ojulari.

Ya bayyana cewa, bayyana manufofi da sassaucin da Gwamnatin Tarayya ta nuna sun bai wa Shell damar kammala raba kadarorin haɗin-gwiwa na ƙasashen waje, waɗanda aka mayar wa Kamfanin Renaissance Africa Energy Company. “Kammala wannan ciniki ya nuna wa duniya jajircewar Shugaban Ƙasa na baiwa masu zuba jari damar saka hannun-jari ba kawai ba, har ma da fita idan ya zama dole – saboda duniyar saka hannun jari tana da ƙarfi sosai”, in ji shi.

Ojulari ya ce nasarar da aka samu wajen rage farashin ya ƙara wa ƙasashen duniya ƙwarin-gwiwa; kuma ya yi tasiri kai-tsaye kan shawarwarin saka hannun jari na Shell a Najeriya.

Ya bayyana cewa Shell ta ɗauki Matakin Zuba Jari na Ƙarshe (FID) na dala biliyan 5 don haɓɓaka filin Mai na Bonga, sannan kuma ta sake zuba jari na dala biliyan 2 a wani aikin haɓɓaka iskar Gas mai zurfi wanda aka sani da HI. “A jimilla, Shell ta riga ta zuba jari sama da dala biliyan 7 tun bayan sanarwar wannan tallafin. Za ku iya fahimtar abin da wannan ke nufi idan aka kwaikwayi irin wannan ƙwarin-gwiwa ga sauran masu zuba jari”, in ji shi.

Shugaban NNPCL ya bayyana cewa Shell yanzu ta tabbatar wa Shugaba Tinubu shirye-shiryen neman sabbin damar saka hannun-jari da darajarsu ta kai dala biliyan 20 a cikin shekaru masu zuwa; wanda hakan zai kara ƙarfafa sha’awar Najeriya a matsayin wurin zuba jari a makamashi.

Ojulari ya kuma bayyana cewa ana cigaba da tattaunawa kan babban aikin Shell na gaba – aikin Bonga South-West – wanda aka ƙiyasta zai buƙaci kashe jari kusan dala biliyan 10, banda manyan kuɗaɗen gudanarwa.

Ya jaddada cewa bayan alƙaluman kuɗi, jarin zai sami fa’idodi masu yawa na zamantakewa da tattalin arziki ga ƴan Najeriya, gami da samar da ayyukan-yi, da kuma farfaɗo da ƙarfin masana’antu na gida.

“Waɗannan manyan alƙaluma suna fassara zuwa ƙarin ayyuka, yayin gini da aiwatar da ayyuka.

Ƴan Najeriya za su sami damarmaki dayawa don shiga; kuma wuraren masana’antu waɗanda suka kasance ba tare da aiki ba na tsawon shekaru saboda rashin ayyuka za su dawo rayuwa”, in ji shi.

Ojulari ya yabawa shugabancin Shugaba Tinubu, yana mai bayyana shi a matsayin mai amfani da tasiri maimakon yin magana mai daɗi, musamman a fannin gaskiya da jajircewa ga shirin gwamnati na ‘Sabuntawa da Fata’.

Ya bayyana fatan cewa ɗorewar manufofi za ta cigaba da buɗe sabbin hanyoyin saka hannun-jari kai-tsaye ga masana’antar Mai da iskar Gas ta Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Malami Ya Zargi DSS da Tauye Masa ’Yancin Kare Kansa a Kotu

‎Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da daukar matakan hana shi cikakken...

Kashe Waɗanda Suka Hallaka Uwa Da ’Ya’yanta a Kano Ya Saɓa Wa Dokokin Najeriya— Babba Lauya a Kano

Wani babban Lauya a Kano ya yi gargadi kan kiran da ake na gaggauta hukuncin kisa kaitsaye ga waɗanda aka kama a Dorayi-Chiranci. ‎ ‎Shahararren lauya a...

Most Popular