Jagoran jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da muƙarrabansa za su yi nadamar barin jam’iyyar a nan gaba.
Kwankwaso ya ce ficewar gwamnan daga NNPP ta bai wa mutane da dama mamaki, har wasu da kan su suna ganin ya yi babban butulci.
“Mutane da dama sun ɗauka wata yarjejeniya ce aka ƙulla tsakanina da shi, ko tsakaninsa da wasu. A wasu lokuta na kan kasa yarda da yadda abubuwa ke tafiya,” in ji Kwankwaso.
