HomeLabaraiCancantar Gwamna Radda Ta Sa Zamu Goya Masa Baya Ɗari Bisa Ɗari...

Cancantar Gwamna Radda Ta Sa Zamu Goya Masa Baya Ɗari Bisa Ɗari a 2027– Hon. Aminu Waziri

-

Hon. Aminu Waziri ya bayyana cikakken goyon bayansa, tare da bada gudummawar neman zarcewar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, yana mai cewa, wannan matsaya ta samo asali ne bayan zurfafa bincike da nazari da suka gudanar kan halin da jihar ke ciki.

 

A cewarsa, binciken ya haɗa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin siyasa daban-daban, ciki har da ’yan adawa da masu mulki, domin tantance yadda ake aiwatar da manufofin Gwamnati da tasirinsu ga rayuwar al’umma.

 

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ya bayyana haka a ranar Asabar 31 ga watan Janairun 2026, a daide lokacin da yake ganawa da Manema Labarai.

 

Hon. Waziri ya ce daga cikin manyan abubuwan da suka ja hankalinshi akwai shirin sabunta birane (Urban Renewal) da gwamnatin Katsina ke aiwatarwa, wanda ya bayyana a matsayin shiri mai tasiri wajen kawo sauyi a birane, ƙarfafa harkokin kasuwanci da matsakaitan sana’o’i, tare da biyan bashin tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya.

 

Ya kuma yi kwatance da wasu jihohin Arewa, inda ya ce Gwamna Dikko Radda na Katsina, Abba Kabir Yusuf na Kano da Dauda Lawal Dare na Zamfara na daga cikin gwamnonin da ke kan gaba wajen aiwatar da manufofin cigaba a yankunan su.

 

Tunda farko, ya taba amince da kasancewarsa cikin haɗakar jam’iyyar ADC, inda Hon. Waziri ya ce idan ana maganar cigaba, wajibi ne a fadi gaskiya, ya ce “daga abin da muka gani, babu wani daga cikin ’yan takarkarin da ke da irin hangen nesa da ingancin shugabanci da Gwamna Dikko Radda ke da shi,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

CAF Strips Senegal of AFCON 2025 Title, Awards It to Morocco

The Confederation of African Football (CAF) has stripped Senegal of the 2025 Africa Cup of Nations (AFCON) title and awarded it to Morocco. In a statement...

Mutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai a Maiduguri

‎Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da mutane 108 suka jikkata sakamakon wasu jerin fashewar bama-bamai da suka auku a daren Litinin. ‎ ‎Rundunar ’yan sandan Jihar...

Most Popular