Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce jami’an sojojin da aka kama bisa zargin yunkurin juyin mulki da aka dakile sun san sakamakon abin da suka aikata.
An kama jami’an sojoji 16, ciki har da birgediya janar da kanar, a watan Oktoban 2025. Daga bisani, Hedikwatar Tsaro ta tabbatar da cewa, an gano shirin kifar da Shugaba Bola Tinubu, wanda aka ce an gano shi ne ta hanyar haɗin gwiwar bayanan sirri daga sojoji, DSS da DIA.
Da yake magana a wata hira da ya yi da TRT World, Musa ya tabbatar da cewa, za a yi wa waɗanda ake zargi shari’a cikin adalci, tare da ba su damar ɗaukar lauya.
Haka kuma, ya ce gwamnati za ta kula da iyalan jami’an da ake zargi.
Musa ya jaddada cewa masu hannu a yunkurin sun riga sun san illar abin da suka aikata, kuma suna shirye su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
