HomeSashen HausaSanya Zaɓen 2027 a Cikin Ramadana An Yi Ne Don Shirya Maguɗi-...

Sanya Zaɓen 2027 a Cikin Ramadana An Yi Ne Don Shirya Maguɗi- Atiku Abubakar

-

Jagoran haɗa ta ADC, Atiku ya buƙaci INEC ta sake duba ranar zaɓen 2027 saboda Ramadan.

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta sake duba ranar 20 ga Fabrairu, 2027 da ta ayyana a matsayin ranar gudanar da zaɓen gaba ɗaya, yana mai cewa wannan lokaci na cikin watan Ramadan lokaci ne na azumi, ibada, da tunani ga miliyoyin musulman Najeriya.

 

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda ya ce sanya zaɓe a tsakiyar watan Ramadan (wanda zai kasance daga 7 ga Fabrairu zuwa 8 ga Maris, 2027) ba kawai rashin hangen nesa ba ne, har ma yana nuna rashin la’akari da halin addini da zamantakewar al’umma.

 

“Zaɓe ba kawai aikin gudanarwa ba ne, amma babban aikin ƙasa ne da ke buƙatar cikakken halarta, juriya, da mayar da hankali na jama’a,” in ji Atiku.

 

“Sanya irin wannan muhimmin aiki a lokacin ibada na musamman yana nuna ƙarancin tunani da rashin fahimtar yanayin addinin mutane wanda lokacin basu da karfin yin zabe a lokacin.”

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma jaddada cewa, a ƙasa mai yalwar ƙabilu da addinai kamar Najeriya, shiryawa cikin haɗin kai da adalci ba zaɓi ba ne wajibi ne.

 

“Abu mai sauƙi kamar zaɓar rana da kowa zai amince da ita bai kamata a yi sakaci da shi ba. Wannan yana nuna ƙwarewa, hangen nesa, da girmama ‘yan ƙasa,” in ji shi.

 

Atiku ya ƙara da cewa idan INEC ta kasa tsara lokacin zaɓe yadda ya dace, to ya dace ‘yan ƙasa su tambaya ko hukumar za ta iya gudanar da zaɓe mai sahihanci, adalci da gaskiya a 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kanwan Katsina Advocates Establishment of FM Stations Across 3 Senatorial Zones Katsina

The Kanwan Katsina District Head of Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara mni, has emphasized the need for continuous training and capacity building for journalists, particularly...

‎Ganduje Ba Shi da Alhakin Sace Dadiyata – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta 8, Shehu Sani, ya karyata zargin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna,...

Most Popular