Wednesday, June 10, 2026
HomeLabarai‎Ganduje Ba Shi da Alhakin Sace Dadiyata – Shehu Sani

‎Ganduje Ba Shi da Alhakin Sace Dadiyata – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta 8, Shehu Sani, ya karyata zargin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi na cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, na da hannu a sace dan gwagwarmayar siyasa, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

‎Shehu Sani ya bayyana cewa wannan zargi ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa babu wata hujja sahihiya da ke nuna cewa Ganduje yana da hannu a lamarin.

‎Ya bayyana hakan a shafin sa na X inda ya gargadi ‘yan siyasa da su guji yin zarge-zarge maras dalili, yana mai cewa irin hakan na iya tayar da hankalin jama’a da kara dagula al’amuran siyasa.
‎Tsohon sanatan ya kara da cewa batun bacewar Dadiyata ya kamata hukumomin tsaro su binciki lamarin ta hanyoyin doka, maimakon jefa shi cikin rigingimun siyasa.

‎Bacewar Dadiyata, wanda ya shahara wajen sukar gwamnati, har yanzu ba a warware ta ba, duk da kiraye-kiraye daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na farar hula da ke bukatar gwamnati ta kara kaimi wajen gano inda yake.

‎Har zuwa yanzu, babu wani rahoto na hukuma da ya bayyana a fili wadanda ke da alhakin bacewar sa, duk da ci gaba da muhawara da ce-ce-ku-ce a bainar jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments